<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><lyrics>[V1]
 1) Mu ƴan yaƙin Yesu ne, gaba mu ke yi
 Shaiɗan ya amsa dā, mun yi bautarsa
 Mutuwar Almasihu fansarmu ta yi.
 Mu yanzu nan gaba binsa za mu yi.

[V2]
 KORUS
 Yaƙin Almasihu, ƴanuwa, mu ke yi.
 Gabanmu ya tafi, binsa mu ke yi.

[V3]
 2) Sarakunan duniya, duk da ikonsu,
 Su kan zo su wuce, ba Su tsayawa,
 Jama'ar Almasihu la tabbata nan.
 Ikon Shaiɗan, ikon duniya, ba sa yin nasara.
 Korus

[V4]
 3) Inda mu ke bi yanzu, sawun mutanen dā.
 Su sun fara shiga cikin hutunsu.
 Mu da su ɗaya ne, duk jama'arsa,
 Ƙaunarmu da saninmu duk da nasu ɗaya.
 Korus</lyrics>
<title>Mu Ƴan Yaƙin Yesu Ne, Gaba Mu Ke Yi LW279</title>
<hymn_number>279</hymn_number>
</song>